31 Maris 2020 - 15:59
Hamas Ta Damke Wasu 'Yan Leken Asirin Isra'ila A Gaza

Dakarun tsaron cikin gida na kungiyar Hamas a yankin Gaza sun sanar da cafke wani adadi mai yawa na jami’an leken asirin HKI a yankin da suke gudanar da ayyukan lekan asiri ta hanyar sa ido da tsegumtawa Isra'ila abubuwan da suka shafi zanga zangar neman komawar yan gudun hijira gida a iyakokin ta da ke gabashin gaza.

(ABNA24.com) Har ila yau dakarun sun watsa bayanai game da daya daga cikin yan leken asirin da aka kama dan shekaru 60 da haihuwa wanda ke yi wa HKI aikin leken asiri tun daga shekara ta 1994, mutumin ya amsa zargin da ake masa na yi wa HKI aikin leken asiri da kuma ya tona asirin sunayen jami’an tsaron Israila da yake aikawa da bayanan sirri.

Daga cikin ayyukan na sa kamar yadda ya bayyana akwai tattara bayanai da suka shafi manyan kwamandojojin gwagwarmayar palasdinu da kuma jamai’an tsaro, da kuma labaran da suke da alaka da zanga – zangar neman dawowar yan gudun hijira gida ga hukumar lekan asirin Isra'ila.

342